An sami mummunan tashin hankali a yankin Yaba dake cikin garin Ondo na jhar Ondo, ya yin da yan fashi da makami su ka farmaki wani bankin yan kasuwa, dake da bai da, nisa da ofishin yan sanda na yankin Yaba.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, Yan bindigan sun afka bankin ne, da misalin karfe 3 na ranan yau Alhamis.
Rahotanni da Jaridar Dimokuradiyya ta tattara, ya tabbatar mata da cewa, Yan bindigan sun yi ta yin harbi kan Mai uwa da wabi, domin firgita mazauna yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadarin Mota ya yi sanadiyar mutuwar masu yi wa kasa hidima 5
Wani shaidar gani da Ido ya tabbatar wa jaridar Dimokuradiyya cewa, muta ne da dama sun sami raunika sanadiyar farmakin da barayin su ka kai bankin.
Akwai Karin bayani…..
A wani labarin Kuma…..
Mummunan hadarin da ya afku jiya Laraba a babban hanyar Abaji zuwa Kwali dake Babban birnin tarayya Abuja, ya yi sanadiyar mutuwar alkalla Matasa masu yi wa kasa hidima guda biyar.
Babbar Daraktar yada labarai da Hulda da jama’a na hukumar ta NYSC, Adenike Adeyemi ta fitar da wata sanarwa Mai taken “Ranar Laraba Mai Muni ga iyalan hukumar NYSC” wato ” Black Wednesday for NYSC Family” a turan ce.
Ta ce, “Cikin jimami da bakin ciki Darakta Janar, da daukacin hukumar NYSC ke jajanta wa, iyalan matasan dake shirin fara bautan kasa, da suka rasa rayukansu a hadarin motan da ya auku, misalan karfe 2 na daren jiya, Laraba, 28 ga Yulin Shekarar 2020, a babban titin Abaji dake Kwali.” Inji sanarwar
“Hakazalika Dirakta Janar da daukacin hukumar na jajantawa gwamnatin jihar Akwa Ibom da na Imo, kan wannan hadarin da ya yi sanadiyar rasuwar matasan masuyiwa kasa hidima.”