Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kaddamar da maharba yan sa kai kimanin 1000 da za su bazama daji don yaki da yan ta’adda.
Da yake musu jawabi a kauyen Khaddamari na karamar hukumar Jere, gwamna Zulum ya jinjina musu bisa irin goyon baya da sune baiwa gwamnatinsa na ganin an wanzar da zaman lafiya.
Gwamnan ya basu amannar taimaka musu ta sigar hanyoyin zamani tare da alkawarin cewa za a rika baiwa kowannen au alawus a wata-wata.
Da ma dai dan Sanata Ahmad Satomi ne ya bada shawara kaddamar da maharban inda juma ba tare da wata-wata ba majalisar dokokin jihar ta amince da hakan don baiwa maharban damar baje irin basirar da Allah Ya huwace musu ta fuskar tsaro.
Tun farko da yake jawabi, Sanata Ahmad Satomi ya ce makasudin bijiro da wannan al’amari shine don taya gwamnatin Jihar yaƙi da ta’addanci, ya ce kuma tuni aka tantance daga hukumomin tsaro dabam dabam a jihar.
Jiher Borno ne da ta kasance cikin tashe tashen hankula tun a shekara ta 2009, inda lamarin ya ki ci ya ki cinyewa, duk da irin ƙoƙarin jami’an soji na dakile matsalar.