By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin teku ne a safiyar ranar Lahadi sun kai hari kan wasu gidajen mai guda biyu, inda suka kashe uku tare da yin garkuwa da ma’aikatan mai bakwai a jihar Bayelsa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya bada labarin cewa ‘yan fashin sun yi awon gaba da wadanda ba su ji ba, basu gani ba inda suka yi musu kwanton bauna a kauyukan Okoroma da Ogbokiri-Akassa na kananan hukumomin Nembe da Brass a Bayelsa.
Majiyoyin dake kusa da gidajen man da abin ya shafa sun ce ‘yan bindigar sun harbe wasu ma’aikatan kamfanin mai na Najeriya Agip Oil da kuma jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) guda biyu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Direban kwale-kwalen nasu, dan asalin yankin Okoroma, har yanzu ba a kai ga gano inda yake ba, kamar yadda majiyoyin yankin da lamarin ya faru suka shaida lamarin ga wakilinmu.
A cewar majiyoyin, a wani harin kwantan bauna da aka yi a Ogbokiri-Akassa dake karamar hukumar Brass, an yi garkuwa da wasu ma’aikatan mai guda shida da ake zargin suna aikin kula dasu ne kusa da dandalin su, tare da yi musu bulaguro.
An kuma bayyana cewa ma’aikatan mai na Agip da jami’an tsaron su sun fuskanci farmaki da misalin karfe 6 na safe a lokacin da suke aiki daf da wani dandali a cikin wata fadama.
Kakakin hukumar NSCDC, reshen jihar Bayelsa, Mista Ogbere Solomon, ya tabbatar da faruwar lamarin a yammacin ranar Lahadi.
Solomon yace jami’an rundunar guda daya ya mutu a harin kwanton bauna, yayin da wasu biyu da suka bace kuma an gano su inda a halin yanzu suna samun kulawa a wani asibitin dake Yenagoa.