Yan gasar tsere na Najeriya sun kafa tarihi
Wakilan Najeriya a gasar tsere ta duniya da za’ayi a kasar Tokyo sun kafa tarihi inda suka kammala tsere mai tazarar mita 400 cikin mintuna uku da sakwanni sha hudu. Jaridar TVCNEWS suka ruwaito.
KaraKAR:-An yankema tsohon shugaban kasar South Africa Jocob Zuma wata 15 a gidan kaso
An sami cimma nasarar ne a wani gwaji da aka gudanar a garin Legas, inda mutane hudu maza da mata sukayi tsere a tazarar mita 100 da mita 400.
Sakamakon ya baiwa kasar Najeriya zama kasa ta sha biyar cikin kasashe sha shida da zasu fafata gasar a kasar Tokyo.
Sai dai wasu maza guda hudu sun rasa gurbin shiga gasar bayan kasa kammala tsere mai tazarar mita 100 cikin sakwanni 38.
Wadanda suka rasa gurbin sune Enoch Edugoke, Usheoritse Itsekire, Jerry Jakpa da Godson Brume.
A ranar ashirin da tara na watan Yuni ne za’a rufe neman gurbin shiga gasar, yanzu dai kungiyoyi hudu daga Najeriya sun sami shiga.
Comments 1