•Sanata Hassan Gusau da ke wakiltar Zamfara ta Tsakiya ya koma APC daga Jam’iyar PDP.
• Sanatan ya bayyana hakan ne a yau Talata a zauren majalissar Dattawan kasar nan.
• Tace rugujewar Dimokuradiyya ta cikin gida ce ya sa ya bar jam’iyar.
Sanatan Zamfara ta Tatsakiya Hassan Gusau ya tsanza sheka daga jam’iyar PDP, zuwa jam’iyar APC Mai Mulki.
Sanata Hassan Gusau dai ya bayyana canza shekar ta shi ne a yau Talata.
Sakon barin jam’iyar ta shi, an karanta ta ne a zauran majalissar Dattawan a yau, wanda Shugaban majissar Ahmad Lawan ya gabatar kafin fara zaman majalissar.
A cikin takaddar da aka gabatar, Sanatan ya bayyana cewa, ya bar jam’iyar ce ta PDP sakamakon rugujewar Dimokuradiyya ta cikin gida a jam’iyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin tarayya ta tsawaita ranar hada katin NIN da layin waya
” Ya ce Ina Mai sanar da majalissa cewa, na fice daga jam’iyar PDP a yau Talata 28 ga watan nan da muke ciki” inji shi.
Kuma “Na yanke shawaran daukan wannan mataki ne, bisa rugujewar Dimokuradiyya na cikin gida daga yanki na, dake jihar Zamfara” inji Sanata.
Mr Gusau shine Sanata na 3 da ya fice daga jam’iyar PDP a majalissar ta 9 mai ci. biyun sun hada da Sanata Elisha Abbo da kuma Sanata Peter Nwaoboshi.
Canza shekar ta shi na zuwa ne, kwanaki uku bayan Bashir Ahmed ya ce gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bar jam’iyar ta PDP zuwa Jam’iyar APC, sai dai har yanzu gwamnan bai bayyana kara cewa, ya bar jam’iyar ba.
Sai dai, idan ba a manta ba a jiya mun kawomu labarin da wani Dan majalissar wakilai dake wakillatar kananan hukumomin Anka da Talatar Mafara wato Kabiru Classic inda ya ce shi ya Nan Daram a Jam’iyar PDP.