Kungiyar Tuntuba ta Arewa wato Arewa Consultative Forum ta ce yan kasa na bukatar a yi musu bayani dalla-dallah gane da jirgin da aka chafke yana safarar abinci da makamai wa ta’adda, don gudun zargi.
Da ma dai an alakanta jirgin da tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar, to sai dai ya fito ƙarara ya karyata wannan zargi.
Cikin wata sanarwa daga mai tallafa mishi kan yaɗa labarai Dakta Yakubu Suleiman ya ce an yi mishi hakan ne da aniyar shafa mishi kashin kaji.
Sai dai cikin wata sanarwa da Kakakin Ƙungiyar ACF Emanuel Yawe ya fitar, ta ce wannan lamari akwai sarkakiya a cikinsa don haka dole hukumomi su fito fili su yi bayani wa jama’a tunda Abdulsalami ya nesanta kan shi da jirgin.
Da ma dai a farkon watan Maris din shekaran Jiya ne Gwamnatin tarayya ta haramta tashi da saukar jiragen sama a jihar Zamfara jim kadan bayan sace ɗaliban makarantar mata ta Jangebe dake jihar.