Wani jami’in soja ya hallaka wani mai saida Kankana a Shataletalen hanyar Zamfra zuwa Sokoto dake cikin garin Zamfara.
Wani shaidar gani da Idanu ya tabbatar wa Jaridar Daily Post cewa bisa ga dukkan alamu jami’in sojan a buge yake bayan ya shawu da barasa, kana ya sayi Kankanar amma kuma ya ƙi biyan shi kudinsa.
“Chacar baki ta kaure tsakanin su, nan ne sojan ya shiga wani Otal dake kusa da wurin da al’amarin ya wakana ya dauko bindiga tare da kiran yan uwansa sojoji kan cewa su biyo shi”
Isar su gurin ke da wuya ne kamar yadda shaidar ya tabbatar, suka fara harbin kan mai uwa da wabi inda nan ne tsautsayi ya faɗa kan Mai kankanar har ya ce ga garin ku.
Mazauna wannan wurin wadanda suka fusata sun yi yunkurin rama wa kura aniyarta, to sai dai an yi rashin Sa’a ya tsere zuwa Otal ɗin da yan uwan shi sojoji suke.
Duk da haka dai ba su daddara ba domin sun yi kokarin kona Otal ɗin, sai dai daga bisani yan sanda sun shiga lamarin inda suka yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar SP Shehu Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce a yanzu haka ana ci gana da gudanar da bincike.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar ya bukaci yan uwan Mamacin da su kwantar da hankalin su kana su bi doka da oda, inda ya tabbatar da cewa za a yi adalci.