Shugaban KAsa Muhammadu Buhari ya kara jaddada aniyar Gwamnatin sa ta ganin bayan masu garkuwa da yan makaranta a fadin kasar nan.
Shugaba Buhari ya jadadda hakan ne a Fadar Gwamnatin sa dake birnin tarayya Abuja yayin da ya tarbi wata kungiya mai rajin kawo daidaito tsakanin jinsi.
“La’akari da tabarbarewar tsaro wanda ya kai ga ana ci gaba da samun wasu miyagu dake sace yan makaranta, zan fada da kakkausar murya cewa gwamnatin mu tana nan daram har sai ta ga bayan wadannan mutane tare da maido da doka da oda” Cewar Shugaba Buhari.
Bari na kara tuna muku, gwamnatin mu a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da kungiyo musamman irin naku wajen ganin an farfado da doka da oda.
A gefe guda kuma shugaba buhari ya bayyana cewa ba za su lamunci cin zarafin wani jinsi ba, don haka ne nan take ya umarci Antoni Janar na Kasa wanda shine Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ministar Harkokin Mata Paulene Tallene da su kaddamar da wani kwamitin ytaki da cin zarafi jama’a wajen ganin an shawo kan matsalar cin zarafin mata da kananan yara.