Gwamna Nyesom Wike na jihar River a ranar Litinin ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su zabi shugaban dake sukar wani sashe ba, a zaben shugaban kasa na 2023 ba.
Wike yace Najeriya bata bukatar mutumin da ya nemi masu zabe kada su zabi dan kabilar Yarbawa ko dan kabilar Ibo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar Adawa A Equatorial Guinea Na Zargin An Tafka Magudin Zabe
Ya yi magana ne a lokacin da ya ke mayar da martani kan laman dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, kan kalamansa na baya-bayan nan.
Atiku ya ce ’yan Arewa na bukatar su zabe shi maimakon dan takarar Yarbawa ko Igbo domin shi dan Najeriya ne da ya zage wurare da dama.
DAILY POST ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana hakan ne a watan Oktoba a wata tattaunawa da kwamitin hadin gwiwa na Arewa da aka gudanar a jihar Kaduna.
Sai dai da yake jawabi a wajen kaddamar da tituna a yankin Emohua na jihar Rivers, Wike ya kuma bayyana dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso a matsayin mutum mai gaskiya.
A cewar Wike: “Bai isa ya ce kar ku zabi dan kabilar Igbo ko kuma dan kabilar Yarbawa ba, amma abin da muke bukata shi ne mu zabip wanda zai kai Najeriya ga ci gaba. Kwankwaso mutum ne mai gaskiya.”
A wani labarin kuma, 2023: Tinubu Na Da Dabarun Tsamo Najeriya Daga Matsin Tattalin Arziki, Jigon APC
Wani mamba a jam’iyyar APC, Olumide Ajiboye ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Bola Tinubu shi ne ya fi cancantar fitar da Najeriya daga durkushewar tattalin arzikin da take ciki.
Ajiboye, wanda memba ne na Kwamitin Yada Labarai a Majalisar yakin neman zaben Tinubu da Shettima ya yi magana a ranar Litinin din nan a matsayin bako a gidan Talabijin na Channels cikin shirin Sunrise Daily.