Akalla ‘yan Najeriya miliyan 15 ne ke cin gajiyar ayyukan samar da ruwan sha a sassa daban-daban na kasar nan.
Ministan albarkatun ruwa, Malam Suleiman Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin nan yayin da yake amsa tambayoyi, a matsayin bako a dandalin kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a Abuja.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Adamu ya ce gwamnati mai ci ta gaji ayyukan da ba a kammala ba a lokacin da ta hau mulki a shekarar 2015.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya kadai ta samar da ruwan sha ga sama da mutane miliyan 15 a cikin ‘yan shekarun nan.
“Saboda haka, bari in fadi haka bisa ga rahoton da ya dace da muka yi kan gwamnatin tarayya kadai.
“Saboda mun gaji ayyuka da dama da ba a kammala ba kamar samar da ruwan sha, ruwan Zungeru-Wushishi, samar da ruwan Zobe, wanda aka fara a 1992.
“Ba a gama ba a lokacin. Amma mun gama shi a karkashin wannan gwamnatin.
“Kusan muna iya gamawa kuma Otta, wanda aikin ya fara a cikin 2003 ko 2004. Shi ma muna aiki a kai.
“Akwai wasu da yawa kamar Takum, Mangu, da sauran ayyuka da yawa. Don haka mun yi aiki da duk wadannan ayyuka don ganin an kammala su,” inji Adamu.
A wani labarin kuma: 2023: Ban Janye Daga Takarar Shugaban Kasa Ba – Tinubu Ya Magantu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya musanta janyewa daga takarar shugaban Kasa.
Tinubu ya saka wani dan gajeren hoton bidiyonsa a kan wani shafi a yammacin ranar Lahadin nan, a wani yunkuri na karyata jita-jitar da ake yadawa.