Wasu masu aikin jigilan fasinjoji a Babur da aka fi sani da ‘yan Okada, sun gudanar da zanga-zanga a Akure babban birnin jihar Ondo a ranar Larabar Nan, inda suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da kisan da wani jami’in dan sanda ya yi wa wani abokin aikinsu.
An ruwaito cewa wani dan sanda da ke gadin gidan mai a unguwar Arakala a Akure, ya kashe wani dan okada da ke zanga-zangar nuna rashin amincewa da mutuwar daya daga cikin mamban su.
Sai dai tun da farko ana kyautata zaton cewa, wata mota da ake zargin na ma’aikatar noma ta jihar ce ta buje Dan Okadan Kuma Direban motar ya tsere. Wanda hakan shine musabbin zanga-zangar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fashewar Iskar Gas ya kashe mutane 5 a Jihar Legas
Kazalika Rahotanni sun ce Bayan Hallaka guda daga cikin yan okadan dan sandan dake zargi da wannan aiki ya gudu.
A kwai Karin bayani…….
Comments 1