Wasu yan sama Jannati huɗu sun dawo wannan duniya lami lafiya, karo na farko kenan tun bayan shekara hamsin da uku.
Mutanen hudu, uku daga kamfanin Jirgin Sama Jannati na NASA da kuma daya daga Kamfanin Jaxa sun shafe watanni shida ne a sama Jannati wato duniyar wata kenan.
Bayan shafe tsawon wannan lokaci, tawagar yan dama Jannatin ta sauka ne a birnin Panama na Jihar Florida dake kasar Amurka.
Kamata ya yi dai a ce mutanen sun yi bankwana da birnin na Florida ba tare da ɓata lokaci ba, to sai dai an samu jinkiri sakamakon rashin kyawun yanayi a birnin.
A yanzu haka matuka Jirgin Kumbon na nan zaman jiran kulawar lafiya gabannin tashi daga birnin Pensacola na Florida zuwa Houston na Texas.
Kumbo na karshe da ya dawo wannan duniya bayan hawa sama Jannati shine Kumbo Apollo eight wanda ya dawo a ranar 27 ga watan Disambar shekarar 1968 bayan shawagi a duniyar wata.