By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Rundunar ‘yan sandan ta cafke wadanda ake zargin ne a garin Odolu da ke karamar hukumar Igamalamela ta jihar tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarauta.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP William Ovye Aya ya rabawa manema labarai a ranar Juma’a, ya ce jami’an tsaro sun fatattaki ‘yan ta’addan daga maboyarsu tare da kama su.
Ya bayyana cewa rundunar ta kwato bindiga kirar Ingilishi guda daya, wayoyin salula bakwai, da kuma laya daga hannun wadanda ake zargin.
Da yake karin haske, Aya ya ce, “Wannan ya biyo bayan rahoton wanda aka yi garkuwa da shi wanda ya tsere daga hannun su a ranar Alhamis 19/5/2022 yayin da ‘yan uwa ke ci gaba da tattaunawa don ganin an sako shi.
Nan take aka tara ‘yan sanda tare da ‘yan banga, mafarauta zuwa cikin daji, da ganin ‘yan sandan, sai ‘yan ta’addan suka bude wuta. A yayin fafatawar da aka yi da bindigar, an kashe biyu, an kama biyu.”
Aya ya bayyana cewa an samu nasarar ne sakamakon dabarun da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Edward Egbuka, ya dauka na dakile ayyukan masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, da sauran miyagun laifuka a jihar.
Ya kara da cewa Kwamishinan yayin da ya yabawa jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga da mafarauta bisa gaggauwa da suka yi don ganin ’yan ta’addan sun gamu da ajalinsu, ya kuma ba jama’a tabbacin cewa ‘yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro. jihar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Aya ya gargadi jama’a da su ci gaba da hada kai da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar ta hanyar ba da sahihan bayanai masu inganci kuma a kan lokaci kan ayyukan masu aikata laifuka.