Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta bayyana cewa sun ‘yanto mutum 26 daga Dungun-Muazu dake karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah shi ne ya bayyanawa ‘yan jarida haka a ranar Laraba a Katsina.
Isah ya ce wadanda aka ‘yanto din sun hada da maza 18 da mata 8. Ya tabbatar da cewa; an sace su ne a ranar 6 ga watan Janairu, a lokacin da ‘yan bindiga sama da 100 akan Babura 50 suka kai hari a kauyen Badna-Buruku dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Isah ya kara da cewa; ‘yan bindigar akan baburan sun kai su zuwa daji a jihar Zamfara.
Ya ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun yi barazanar hallaka wadanda suka kama idan har ba a ba su naira miliyan daya ba ga duk wanda suka kama.
Ya tabbatar da cewa jami’ansu da suka fita aiki a dajin Dungun-Muazu dake karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina ne suka ‘yanto su.