‘Yan sanda a jihar Jigawa sun gano wata Budurwa mai suna Ruqayya ‘yar shekara 22 da ta bace a karamar hukumar Kiyawa. Kamar yadda DAILY POST ta ruwaito.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ya sanyawa hannu kuma ya bayyawa manema labarai ciki har da majiyar Dimokuradiyya.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Nada Charles III A Matsyain Sabon Sarkin Austiraliya Da New Zealand
Ya ce rundunar ‘yan sanda ta samu rahoton cewa an gano wata mata a makale a ranar 09/09/2022 da misalin karfe 2:00 na dare a Shuwarin Main gadar sama da ke karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.
Shiisu ya ce bayan samun rahoton, ‘yan sandan sun garzaya yankin inda suka dauko Budirwar.
Ya kara da cewa, matar ba ta tuna komi ya faru da ita ba a lokacin da ake yi mata tambayoyi, inji shi.
Rundunar ‘yan sandan ta bukaci jama’ar da suka iya gane ta, ko ‘yan uwanta, da su kai je ofishin ‘yan sanda na Shuwarin ko kuma ofishin ‘yan sanda na Kiyawa.
A WANI LABARI KUMA: Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 3, Tare Da Lalata Gidaje Sama Da 1, 000 A Bauchi
Babban Daraktan Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Bauchi, Dakta Ibrahim Kabir, ya tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon ambaliyar ruwa da ta lalata gidaje 1,453 da gonaki da dama a kananan hukumomin Zaki da Gamawa.
Kabir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Gwamna Bala Mohammed yayin da ya kai ziyarar jajantawa al’ummar da abin ya shafa a ranar Asabar a karamar hukumar Zaki.