Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi ‘yan siyasa da su kaucewa kalaman barazana dangane da zaben da za a sake na ‘yan majalisar tarayya a jihar.
Habu Ahmadu-Sani, Kwamishinan
‘yan sandan jihar shi ne ya bayyana hakan a yayin zaman da ya gudana tsakanin ‘yan
sanda da masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaro a Hedikwatar ‘yan sanda dake
Bompai a Kano.
DSP Abdullahi Haruna, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a garin Kano a ranar Alhamis.
“Duk wanda muka kama yana yiwa zaman lafiyar jihar barazana sakamakon sake zaben ‘yan majalisa zamu dauki mataki akansa bisa doka.” In ji sanarwar.
Ya tunatar da dukkanin masu ruwa da tsaki da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar da za a yi zaben da su kan hannu da suka sanya kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta na INEC, Farfesa Riskuwa Shehu, ya ce hukumar ta su ta shirya gudanar da sahihin zabe a zaben da za a sake.
Ya ce tuni suka kammala shirya dukkanin kayayyakin zaben da za a sake a kananan hukumomin Rogo, Bebeji, Kumbutso, Kiru, Minjibir, Tudun Wada, Madoi, Bunkure, da kuma Doguwa a jihar.
Har wala yau zaman ya samu halartar shugabannin tsaro a jihar.