Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta sha alwashin cafke wanda ya kashe wata yarinya ‘yar shekaru 14, Maryam Salisu, wadda aka kashe a ranar Talatar makon jiya a wajen kauyen Babale da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Batholome Onyeka, wanda ya samu wakilcin jami’in ‘yan sanda mai kula da reshen Nassarawa Gwong, SP Musa Hassan, ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci gidan iyalan marigayiyar
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Umarnin Rufe Gadar Tiga Dake Kano
Daily Trust ta ruwaito a ranar Alhamis din da ta gabata yadda aka kashe marigayiyar tare da cire wasu muhimman gabobinta bayan ita da wasu ‘yan mata 12 sun je debo wa iyayensu itace.
Mai magana da yawun iyalan, Fatima Danliti, ta godewa ‘yan sanda kan damuwarsu da lamarin.
Da yake mayar da martani a madadin al’umma, hakimin riko, Aminu Maisamari, ya roki ‘yan sanda da su tabbatar da cafke mai laifin.
Sai dai DPO ya gargadi mazauna yankin da su daina tura yara daji ko gonaki, musamman ganin yadda babban zaben shwkarar 2023 ke kara karatowa.
A WANI LABARIN KUMA: .Yan sanda Sun Kashe Wani Kasurgumin Dan ta’adda A Jihar Kataina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kashe dan ta’adda guda daya, tare da kwato bindiga kirar AK-47 daya da babura guda hudu da maharan ke amfani da su wajen kai hari a unguwar Mararabar Yakawada da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Katsina SP Gambo Isah, “’yan ta’addan da ba su wuce 30 ba, a kan babura sun tare hanyar Sabuwa zuwa Mararabar Yakawada da nufin yin fashi da garkuwa da mutane.