Ministan Albarkatun Ruwa, Alhaji Suleiman Adamu, ya yi kira da a rufe Gadar Sarkin Kogi da ke Tiga dna karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano ga masu ababen hawa da masu tafiya a kasa domin kare lafiyarsu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Adamu ya yi wannan kiran ne a wata ziyarar aikin tantance madatsar ruwa ta Tiga da Bagauda tare da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 200 A Makurdi
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamna Hassan Fagge ya fitar ranar Laraba a Kano.
Ministan ya bayyana cewa malala a madatsun ruwan biyu , na aiki yadda ya kamata sabanin jita-jita.
Ministan ya ce, ambaliyar ruwan ba ta shafi madatsun ruwa na Tiga da Bagauda ba, ya kara da cewa ruwan dam din bai bai yi karuwar wuce kima ba.
Ya umurci hukumar raya rafin Hadejia Jama’are da ta ci gaba da kula da madatsun ruwa a yau da kullum.
Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Nasiru Gawuna, ya bada tabbacin aniyar gwamnati na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummarta.
Gwamnan ya bayyana ziyarar a matsayin nuna damuwar da gwamnatin tarayya ke ci gaba da nunawa kan jihar.
Don haka ya mika godiyarsa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hannun Ministan kan yadda ya mayar da martani a kan lokaci.
Idan dai ba a manta ba a makon da ya gabata ne ambaliyar ruwan Tiga ta lalata filayen noma da tituna da gidaje tare da raba mazauna yankunan da muhallan su.
A WANI LABARIIN KUMA: Yan sanda Sun Kashe Wani Kasurgumin Dan ta’adda A Jihar Kataina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kashe dan ta’adda guda daya, tare da kwato bindiga kirar AK-47 daya da babura guda hudu da maharan ke amfani da su wajen kai hari a unguwar Mararabar Yakawada da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.
A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Katsina SP Gambo Isah, “’yan ta’addan da ba su wuce 30 ba, a kan babura sun tare hanyar Sabuwa zuwa Mararabar Yakawada da nufin yin fashi da garkuwa da mutane.