Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama wasu sojoji biyu da ake zargi da kashe wani shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami da aka kashe a ranar Juma’a da misalin karfe 9 na dare.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa an Harbe malamin ne a kan hanyarsa ta zuwa Gashua daga Kano.
Wasu majiyoyin sirri da dama sun yi zargin cewa sojoji sun kashe malamin ne bayan da ya rage musu hanya daga shingayen binciken sojoji na Nguru zuwa Jaji-maji, da ke kusa da karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe.
KARANTA ANAN: Kwankwaso Yayi Alkawarin Magance Matsalar Tsaron Najeriya Idan Har…
Majiyar ta ce an harbe shi ne sanda suke tafiya, kuma daga bisani sojojin suke tsere da motar sa kirar Honda Accord, kafin daga bisani ‘yan sanda su kama su.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya ce sojojin biyu da aka kama su ne Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon na 241 Recce Battalion, Nguru, jihar Yobe.
Ya ce an kai mutanen biyu zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar da ke Damaturu domin gudanar da bincike.
An yi jana’izar fitaccen malamin nan ne a ranar Asabar a garin Gashua da ke Jihar Yobe a yayin da dubban dalibansa da ‘yan uwa da abokan arziki suke ta jimamin mutuwarsa.
A wani labarin kuma: Jami’an Yan Sanda Sun Gudanar da Zanga Zanga a Jihar Kwara
Kimanin matasa 1,056 da aka dauka aiki a matsayin Constabulary a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya domin baiwa ‘yan sanda damar tabbatar da tsaro a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zanga a Ilorin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Zanga zangar ta biyo bayan rashin biyansu albashin watanni 16 da gwamnatin jihar tayi.