By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun, a ranar Lahadi, tace ta kama wani Sajandin dan sanda da ake zargi da harbe wani direba har lahira a Unguwar Kobogbogboe/Ota-efun dake Osogbo ranar Juma’a.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Yemisi Opalola, ya fitar, yace za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala shari’ar ‘yan sanda cikin tsari.
Ya ce kama wanda ake zargin tare da tsare shi wani bangare ne na kokarin hukumar na dakile duk wani nau’in rashin da’a da ayyukan rashin da’a.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Rundunar ‘yan sandan Osun ta kama tare da tsare dan sandan, Sajan Moses Samuel, wanda ya harbe wani mai suna Malam Kabiru Babai’ mai shekaru ’33, a ranar Juma’a, 3 ga watan Disamba a kewayen Kobogbogboe / Ota-efun, dake Osogbo.
“An fara bincike tare da ladabtarwa kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala shari’ar ‘yan sanda cikin tsari’.
“Wannan muna fatan zai zama hana wasu jami’an ai kata irin sa Anna gaba.
“Kwamishanan ‘yan sanda, Olawale Olokode, yace zaiyi amfani da wannan kafar wajen bayyana ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin,da abokan aikin sa,
“Olokode ya kuma yi addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan lamari na rashin tausayi.
Sannan ya kuma tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci.” a cewar Sanarwar.