Rahotanni sun ce an kashe wasu mutane shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar Laraba a wani artabu da ‘yan sanda a garin Benin, babban birnin jihar Edo.
Rahotannn sun Kuma bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tare wata motar bas mai mutane 18 da ta taso daga Legas zuwa Gabashin kasar nan a kan titin Legas zuwa Benin ta hanyar Legas.
An dai ce suna kwashe wadanda abin ya rutsa da su cikin dajin ne a lokacin da suka gamu da ‘yan sanda suka yi artabu da su.
Kazalika an bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun mutu ne sakamakon raunukan da suka samu a yayin fafatawar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana kyautata zaton wadanda suka mutun na cikin gungun ‘yan ta’addan da ke addabar babbar hanyar Benin zuwa Lagos da kewaye, inda suke garkuwa da masu amfani da hanyar.
Ya ce likitocin da ke bakin aiki a asibitin sun tabbatar da mutuwar masu garkuwa da mutanen.
Bello ya ce an kubutar da fasinjojin ne ba tare da sun ji rauni ba yayin da ake ci gaba da bibiyar dajin domin kamo wasu ‘yan kungiyar da suka gudu.