Hukumar ‘yan sanda a ranar laraba ta ce dalibai 5 a ka kashe a jami’ar jihar Kogi da ke Ayingba ba 13 kamar yadda yake ta yawo a kafafen yada labarai. Kakakinn rundunar ‘yan sandan jihar, William Aya ne ya bayyana haka a garin Lokoja.
A cikin wata sanarwa, Kakakin ya ce daga cikin wadanda aka kashe din akwai Justice Keke,dalibi dan aji 3 dake karatu a tsangayar koyon sarrafa sinadari wanda ya hanyar tafiya gida ne daga makaranta abi ya rutsa da shi a ranar 1 ga watan Nuwamba.
Ya kara da cewa, a ranar 2 ga watan Nuwamba a tsinci wani gawan da ba a iya tantance ko waye bane wani kango da ke bayan jami’ar.
Kakakin ‘yan sandan ya akwai Abdulrahman Usman, dalibi dan aji 2 a sashen tarihi, wanda aka kasheshi a gidan mahaifinshi a ranar 3 ga watan Nuwamba.
Ya kuma ce, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Akeem Busari ya yi kira da mutane da su yi watsi da labaran karya kuma su rika kokarin yadda za a samar da zaman lafiya dauwamammiya.
Busari ya ce rundunar ta shirya don tabbatar da tsaro don kowa ya fito ya kada kuri’arsa a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Ya kuma lashi takobin hukunta duk wani dan daba ko dan jagaliyar da zai yi kokarin tada-zaune-tsaye a lokacin zaben.