Rahotanni dake shigowa Jaridar Dimokuradiyya na nuni da cewa jami’an tsaron ‘yan Sandan Nijeriya sunn afkawa ‘yan shi’a masu muzaharar ganin an saki jagoransu, Shaikh Ibraheem Zakzaky a Abuja.
Masu muzaharar dai kamar kullum yadda suka saba, a yau Talata sun fara muzaharar ne daga Sky memorial, inda suka nufi gadar Berger daka cikin birnin tarayya Abuja.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa; ‘yan sanda sun harba tiya gas a yayin da kuma suka yi amfani da harsasai masu rai kan masu muzaharar. Inda bayanai daga bangaren ‘yan shi’ar suka ce an raunata musu mabiya biyar, a yayin da ya zuwa hada wannan rahoton ‘yan sandan ba su ce uffan ba dangane da lamarin.
Su dai masu muzaharar ne wanda mafi yawansu matasa ne, sun fito maza da mata, inda suna me kira da gwamnati ta saki jagoransu kamar yadda kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta nema tun cikin shekarar 2016.