Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta rufe wani gidan mari na Malam Bello Mai Almajirai a yankin Daura, inda ta ce an sanya fiye da mutum 360 cikin wani mummunan hali da azabtarwa tsawon shekaru.
Wannan ne gidan da ake zargin ana azabtar da mutane na biyu da hukumomi suka ce sun gano kasa da wata guda a arewacin Nijeriya.
Sama da mako biyu ke nan da ‘yan sanda suka rufe makamancin wannan gida tare da kubutar da gomman daurarru a jihar Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar ‘ya sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya shaida wa BBC cewa wata hatsaniya ce ta kaure a cikin gidan, kawai sai yaran suka fara dirgowa ta katanga da kafafuwansu daure da mari ko sarka.
”Yaran sun cika cikin gari ne, lamarin ya tayarwa da jama’ar Daura hankali, ganin su da sarka kamar lokacin cinikin bayi. Kuma akwai yara kanana ‘yan shekara bakwai zuwa takwas har da manya ‘yan shekara 40. Sun yi korafin azabtar da su ta hanyar lakada musu duka, ko sallah idan za su yi sai an ga dama a ke kwance su”, in ji SP Gambo.
SP Gambo ya ce akalla akwai mutane sama da 300 a wannan gidan, to amma saboda tserewar da wasu daga ciki suka yi mutum 60 kadai jami’an tsaron suka samu kubutarwa.
Yaran dai sun yi korafin wadanda suka girme su, su na ba su wahala har da ikirarin mazan na lalata da su kamar yadda suka shaida wa ‘yan sanda.
Gidajen mari ko horo kamar yadda wasu suka fi daukarsu, iyaye ko ‘yan uwa kan kai yaron da ake ganin yana neman kangarewa ko mara jin magana da nufin ladabtar da shi. To amma daga bisani labaran da ke fitowa ba masu dadi ba ne.
SP Gambo ya ce shi kan shi Malamin wannan makaranta yana hannunsu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da duk wanda aka samu da laifin lalata da ko azabtar da yaran gaban shari’a.