By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a Najeriya tace ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi‘ yan fashi ne masu ba da bayanai, sannan kuma sun ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su.
SP Gambo Isah, kakakin rundunar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Talata a Katsina.“Inda yace ko a ranar 20 ga Satumba, 2021, Rundunar ta yi nasarar cafke wani matashi dan shekara 30 daga Sabon Garin Faguwa, Karamar Hukumar Dutsinma wanda ke zaune a cikin dajin.
Sanannen kwamandan ‘yan fashi ne a ƙarƙashin jagorancin Sani Muhidinge, wanda ke cikin jerin sunayen da ‘yan sanda suke nema ruwa a jallo.”Haka kuma, mun kama wani shahararren dan fashi mai shekaru 22 na Mai Gezoji, Tashar Mai Alewa, Karamar Hukumar Danmusa.
“Gaskiyar lamarin ita ce, a ranar 15 ga watan Satumba, 2021, wasu ‘yan bindiga masu yawa da tafe a kafa, suna harbe harbe da bindiga AK-47, sun kai hari kauyen Kitibawa dake karamar Hukumar Dutsinma inda suka kashe mutane biyu, tare da kwasar kayan shago da kuma yin garkuwa da mata 18 da jariransu bakwai.
Sannan muna samun rahoton, Kwamandan Yankin Dutsinma, ACP Aminu Umar, ya jagoranci tawagar Yan Sanda zuwa yankin, inda suka tare yan fashin sannan suka yi artabu da su.
A cewar Isah, yayin gudanar da bincike kuma bisa sahihan bayanan sirri da muka samu a ranar 20 ga watan Satumba, 2021, Rundunar ta kuma yi nasarar cafke wani mutum mai shekaru 45 da ake zargi a Tashar Mai-Alewa, dake Karamar Hukumar ta Danmusa.
Ya kara da cewa, an kama wani mutum mai shekaru 34 da wannan adireshin, wani ma’aikacin lafiya da ake zargi yana bada magani ga ‘yan bindiga, “Wadanda ake zargin sun furta aikata laifin, kuma har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike,” in ji shi.