‘Yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a ranar Litinin din nan sun halarci babban taron kungiyar lauyoyin kasa da ke gudana a Legas, kamar yadda gidan talabijin channels ya bayyan.
Peter Obi na jam’iyyar Labour da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP sun bayyana da kansu a wurin taron.
Karanta kuma: Shugaban Kasa: Dalilin Da Ya Sa Peter Obi Ya Fi Atiku, Da Tinubu – Shugaban Yarabawa
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, NBA ta ce wasu ‘yan takarar shugaban kasa biyu – Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ba su tabbatar da halartar taron ba.
Babban taron shekara-shekara na NBA na 2022, mai taken “Tsarin Canji”, za a ci gaba da gudanar da shi a Eko Atlantic City har zuwa 26 ga watan Agusta.
A wani labarin kuma: Yan Takarar Shugaban Kasa Na Yankin Kudu Maso Gabas Na Ganawar Sirri
Ta ron na sirri wanda ke gudana a gidan sirri na tsohon gwamnan jihar Imo a Abuja, Rochas Okorocha, an fara shi ne da misalin karfe 3:45 na rana.
Duk da cewa har yanzu ba a bayyana Makasudin taron ba, amma wani mai taimaka wa Okorocha da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa cewa taron ya ta’allaka ne kan yadda za a zabi dan takarar da ya dace a shiyyar.