Kungiyar bada agajin gaggawa ta Red Cross ta ce, Akalla mutane 30 ne suka rrasa rayukan su cikin kwanaki biyu, sanadiyar wani farmaki da Yan bindiga suka Kai a Gabashin Jamhoriyar Dimokuradiyyar Congo.
Lamarin dai ya faru ne a lardin Ituri dake makwaftaka da Arewacin Kivu dake ci gaba da fuskantar hare-hare, lamarin da Gwamnatin kasar ke kokarin dakile ayyukan kungiyoyin tada kayar baya.
A na dai kyautata zaton cewa, kungiyar Yan aware ta ADF ce ta kai harin, daya daga cikin kungiyoyin yan tawayen da ke cigaba da kai munanan hare-hare a yankin.
Kungiyar dai na gudanar da ayyukanta ne cikin rashin Imani, yayin da aka tsinci wasu gawarwaki a daure, wasu Kuma an musu yankan rago.
A yayin harin an babbaka wa gidaje da dama wuta, tare da sace dukiyoyin al’umar da lamarin ya rusta da su.
A dai watan Disamban bara, fiye da Sojin Uganda Dubu daya ne suka ka tsallaka DR Congo a wani aikin soji na hadin guiwa, domin fatattakar Yan kungiyar ADF.