Akwai ‘yan wasa da dama da za a ga cewar idan suna fafata wasa a wata ƙungiyar ƙwallon ƙafan cewar sun fito daga ƙasa guda wato mahaifarsu guda kenan, yayin da idan wasu suna buga wasa kamar mutane biyar a ƙungiyar ƙwallon ƙafa guda ɗaya. Amma kuma wasu ‘yan wasan sai su kwashi shekaru batare da ka gansu a ƙungiyar ƙwallon ƙafa guda ba wanda suke a matsayin ‘yan ƙasa ɗaya.
Babban misali a nan shine zaka iya ganin ‘yan wasan ƙasar Brazil kamar guda 3 ko 4 ko 5 ako wanne manyan league da ake dasu guda biyar kuma a ƙungiyar ƙwallon ƙafa guda suna fafata wasansu, idan anyi duba a Real Madrid akwai Cassemiro da Marcelo da Vinicious da Rodrygo dukkaninsu ‘yan ƙasar Brazil ne, haka a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal akwai Willian da David Luiz da Martenelli da Gabriel da Pablo Wanda dukkaninsu ‘yan Brazil ne.
Haka zalika zaga iya ganin jerin ‘yan wasa kusan mutane 11 duk ‘yan ƙasa ɗaya a ƙungiyar ƙwallon ƙafa guda ɗaya amma kuma mafi akasari zakaga hakan tana faruwa idan akace ita ƙungiyar ƙwallon ƙafan duk ‘yan asalin ƙasar da ƙungiyar take a zaune ne wato kamar ace ƙungiyar ƙwallon ƙafan a Andalus take kuma suma ace jerin ‘yan wasa kamar 11 dukkanisu ‘yan ƙasar ta Andalus ne.
Amma kuma wani abu ya faru a ƙasar Ingila a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wolverhampton Wonders Inda aka sami ‘yan wasa guda coma rigis wanda dukkaninsu ‘yan ƙasar Portugal ne amma ita kuma kama ƙungiyar ta Wolverhampton a ƙasar Ingila take. Inda a halin yanzu itace ta tara ‘yan wasan kuma wannan ba ƙaramin tarihi bane ta ajiye.
Ga jerin sunayen ‘yan wasan na ƙasar Portugal da suke a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wolverhampton Wonderers:
Nelson Samedo.
Ruben Naves.
Bruno Jordao.
Pedro Neto.
Joao Moutinho.
Ruben Vinagre.
Daniel Podonce.
Fabio Silva.
Roderick Miranda.
Rui Patricio.
Idan mun dawo tarihin da ‘yan wasan ƙasar ta Columbia suka kafa a gasar Firimiya ta bana ‘yan wasan dai suna fafata wasansu a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton wato Yerry Mina da James Rodriguez Inda suka kafa tarihin a wasan da Everton ta doke Brighton daci 4 da 2 a wasan mako na 4 na sabuwar kakar gasar ajin Firimiya da aka fara tun a watan da ya gabata.
Tunda aka fara fafata gasar ajin Firimiya shekaru aru-aru abune mai wahala kaga ‘yan wasan ƙasar Columbia suna buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa guda ɗaya tare, hasali ma ‘yan wasan ƙasar ta Columbia basu fiye zuwa suna buga gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila ba, amma yanzu gashi an samu a Everton inda James Rodriguez da Yerry Mina suke a tare inda kuma suka kafa tarihi a jiya.
Tarihin da suka kafa shine tunda aka ƙirƙiri gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila ba a taɓa samun ɗan wasan ƙasar Columbia ya taimakawa ɗan Columbia ya zura ƙwallo a raga ba amma a jiya James ya taimakawa Yerry Mina ya jefa ƙwallo a wasan da suka sami nasara daci 4 da 2, haka zalika a wasan shina James Rodriguez ya jefa ƙwallaye guda biyu daga cikin ƙwallaye guda huɗun da aka jefa.
Sakamakon wannan nasara da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Everton ta samu yasa taci gaba da jan ragamar teburin gasar ta Firimiya inda take da maki 12 bayan data lashe dukkanin wasanninta guda huɗu inda suka lashe ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Tottenham da West Brom da Crystal Palace da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brighton And Hove Albiol.