Gwamnatin Tarayya ta bada wata masaniya akan yadda ta ajiye wasu matakai domin yaƙi da cin hanci, gami da kwato kuɗaɗen da aka sace, wanda hakan ya sanya aka samu nasarar dawo da wasu kuɗaɗen da aka sace a ƙasar.
Waɗannan kuɗaɗe sun ƙunshi Dala Miliyan $322.52 daga ƙasar Switzerland, da Dala Miliyan $311.7 daga ƙasar Amurka, da Euro miliyan 5.4 daga ƙasar Northern Island, gami da euro Miliyan 4,214,017.66 da kuma Dala Miliyan 200 daga ƙasar Ingila.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kashe Uwa Da Danta Dan Shekara 2 A Jihar Delta
Attoni-Janar kuma Ministan Shari’a a cewar wata sanarwa da Mai Taimaka masa akan Kafafen Yaɗa Labaru Dr Umar Gwandu, ya bayyana haka a lokacin wata Lakca da cibiyar kafafen yaɗa labaru da zaman lafiya ta New York, ƙasar Amurka ta shirya a ranar Litinin.
Acewar da kasancewar ɗaukar tuta na Afirka akan yaƙi da cin hanci, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya maida hankali domin yaƙi da cin hanci da dukkanin ƙarfin sa, ta hanyar bin matakin Shari’a.
Yace kuɗaɗen da gwamnati ta ƙwato a ƙasashen waje zai taimaka wajen baiwa ƙasashen Afrika damar yaƙi da matsalar.
Malami yace ” an ɗauki matakai da dama na shari’a, da Hukumomi da Tsare-tsare domin yaƙi da cin hanci, da tabbatar da nagartaccen shugabanci ga ƴan ƙasa.