Yanzu Kowa So Yake in tsaya takara a 2024 – Donald Trump
Donald Trump ya sake wani jawabi kan yaƙin neman zaɓe na shiga fadar White House a shekarar 2024, inda tsohon shugaban na Amurka ya shaidawa gidan talabijin na Indiya cewa, tsayawa takara zai farantawa mutane da yawa farin ciki.
“Kowa yana so in tsaya takara. Ni ne ke kan gaba a zaben,” in ji Trump a wani bangare na wata hira da NDTV tayi dashi a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Kasawar APC ba zai sa Gwamnonin PDP da basu yi aiki su samu Ƙuri’u ba — Wike
“A kowane zabe, Jam’iyyar Republican da na Democrat, kuma zan yanke shawara nan gaba kadan, akan wadda zan shiga. Kuma ina tsammanin mutane da yawa za su yi farin ciki sosai, ”in ji shi.
Attajirin tsohon tauraron ta Reality TV mai shekaru 76, ya kuma sake maimaita ikirarin cewa zaben 2020 da ya sha kaye a hannun Shugaba Joe Biden an tabka Maguɗi.
“Akwai babbar hujja, akwai kwararan hujjoji,” in ji Trump.
Dan jam’iyyar Republican ya fuskanci shari’a mai tsanani kan kokarin da ya yi na soke sakamakon zaben da kuma harin da magoya bayansa suka kai kan babban birnin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun bara.
Tun da ya bar mulki, ya kasance mai raba kan Amurka, yana ci gaba da shuka karya cewa ya lashe zaben.
A halin yanzu dai ana gudanar da bincike a kansa kan yiwuwar karkatar da wasu takardu na sirri, inda hukumar FBI ta kai farmaki gidan sa na Florida a watan jiya.
Trump ya musanta aikata ba dai-dai ba, ya kuma kira harin “daya daga cikin munanan hare-haren da ake kaiwa dimokradiyya a tarihin kasarmu”.
A wani jawabi da ya yi ranar Asabar a Pennsylvania, ya mayar da martani ga ikirari da Biden ya yi cewa shi da magoya bayansa suna zagon kasa ga dimokuradiyyar Amurka, yana mai kiran Biden a matsayin “makiyin ƙasar”
A wani labarin kuma: Jam’iyyar PDP za ta Ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman Zaɓen Shugaban Ƙasa
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce nan ba da dadewa ba zata bayyana jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023.
Sakataren yada labarai na kasa Debo Ologunagba ya bayyana haka ga Manema Labarai a daren Laraba bayan wani taron kungiyar ‘yan Majalisar Tarayya a Abuja.