Bisa ga dukkan alamu dai dangantaka tsakanin Jaruman finafinan Hausa na Kannywood wato Zahraddeen Sani da Ummi Zee-Zee na ci gaba da kara tsami.
A kwanakin baya ne dai Jaruma Ummi Zee-Zee ta bayyana aniyar ɗaukar rayuwar ta sakamakon abinda ta kira ɗacin duniya a gareta.
To sai dai jarumar ta gamu da fushin al’ummar duniya musamman ma’abota shafukan sada zumunta na zamani inda a nan ne ta wallafa wancan aniya tata.
Daga cikin jama’a da suka yi ta sukar ta harda abokin aikinta wanda shi ma ya yi shura a masana’antar ta Kannywood wato Zahraddeen Sani, inda ya bayyana cewa ta yi ne kawai ne don a rika tunawa da ita duba da yadda duniya ta yi mata tsami.
To sai dai jarumar ta fito ta yi maganganu masu tsauri da suka haɗa da na gori, wanda ake ganin martani ne ga batun Zahraddeen Sani, duk da cewa ba ta fito fili ta kira suna ba.
Amma bayan wancan kachaniya da auku a tsakanin Jaruman biyu ne sai aka ji shiru tamkar an shuka dusa.
Sai dai a yau jama’ar Najeriya sun wayi gari da wani sabon al’amari da ya nuna cewa akwai tsamin dangantaka tsakanin su, kamar yadda jaruman ta bayyana a shafinta na Instagram.
Cikin wani hotonta da abokin aikin nata, Ummi Zee-Zee ta bayyana cewa har yanzu fa akwai gaba tsakaninsu, kalmar da ba ta yi wa wasu mabiyanta daɗi ba.
“Wani hoto mai ratsa zuciya ni da Zahraddeen Sani gabannin aminai su zamo abokan gaba, yayin taron gangamin yaƙin neman zaben Atiku Abubakar a Kaduna, haka rayiwa take” Cewar Ummi Zee-Zee.
Wata kila dai za a iya ɗora kalaman Zahraddeen Sani a mizani ya iya zama alkali ga cewa Zee-Zee na buƙatar farfaɗo da komadarta ne da ya larme, ganin cewa ta nuna shakuwarsu a baya.