Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun hallaka tsohon Kwamishinan yan sanda kuma mai babban mai baiwa gwamnan Jihar Binuwe shawara kan tsaro Dega Chris.
Maharan sun yi kwantan bauna ne wa Dega a birnin Jos na Jihar Pilato a daren ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa gabannin hallaka tsohon Kwamishinan yan sandar, sai da yan bindigar suka yi mishi luguden wuta, kafin daga bisani ya ce ga garinku.
Kwamishinan yan sandar Jihar Pilato Edward Egbuka ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce harin na kwantan bauna ne.
Ya ce tuni kuma aka kama mutane da dama da ake zargi da hallaka tsohon Kwamishinan yan sandar.