Tsohon Gwamnan Jahar Ekiti Chief Segun Oni, yace samun nasarar gudanar da zaɓen shuwagabannin Jami’iyyar PDP na Ƙasa, wata alama ce dake nuna cewa Jam’iyyar PDP ta dawo da ƙarfin ta, kuma ta shirya ceto Najeriya.
Oni ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi a Abuja.
Ya bayyana samun sabbin shugabannin PDP a matsayin wani cigaba a jamiyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Akalla Mutane Tara Ne Suka Mutu Biyo Bayan Harin Bam Da Aka Kai A Kasar Yamen
“A matsayin ta na Jam’iyya, a shirye muke muyi aiki da ƴan Najeriya, domin taimakawa ƴan Najeriya su fita daga ƙangin talauci da rashin tsaro, wanda ba wanda bai shafa ba.
“Muna faɗi da babbar murya cewa, mun yi koyi da kura-kuran da muka yi a baya, kuma an sanya mu gane cewa sai mun yi ƙoƙari domin ceto al’umma,” inji shi.
Oni ya taya murna ga Shuwagabannin Jam’iyyar PDP, da Gwamnoni, da ƴan Majalisu, da dukkanin mambobin jami’iyyar wajen samun nasarar gudanar da zaɓen na ƙasa.
Ya kuma taya sabon shugaban murna da sake zaɓar shi da aka yi a matsayin shugaban jam’iyar Sanata Iyorchia Ayu, da sauran shuwagabannin da aka zaɓa.
Oni ya buƙaci mambobin jami’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki akan samun nasarar gudanar da zaɓen, ta hanyar jefar da bambance-bambance tare da aiki tare domin cigaban jamiyyar.