Wasu Hare -haren abubuwa masu fashewar sun tarwatsa masallacin ‘yan Shi’a a garin Kandahar da ke kudancin Afganistan yayin sallar Juma’a, inda suka kashe akalla mutane 32 tare da jikkata wasu 53.
Ba a bayyana musabbabin fashewar bama-baman ba a yauJuma’a, amma hakan na zuwa ne mako guda bayan harin kunar bakin wake da aka kai kan masu ibada na Shi’a a wani masallaci dake birnin Kunduz da ke arewacin kasar, wanda kungiyar Daesh ta yi ikirari Kai harin daga bisani.
“Ya zuwa yanzu an kawo gawarwaki 32 da mutane 53 da suka jikkata zuwa asibitin mu,” kamar yadda wani likita a babban asibitin Mirwais na birnin ya shaida wa Kamfanin dillancin labarai na AFP.
Wasu majiyoyin daga Masana kiwon lafiya a kasar, da wani jami’in lardin sun tabbatar da adadin sama da mutane 30 da suka Mutu a harin, kuma a kalla motocin daukar marasa lafiya 15 sun ruga da sun isa wajen da lamarin ya afku.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP ta Kara wa’adin Saida Fom na Yan takarar Kujerar Gwamnan a zaben Anambra
A gefe guda Shafin Facebook na masallacin ya yi roƙon ba da gudummawar jini ga wadanda harin Bama-Baman ya shafa.
Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ya ji karar fashewar abubuwa guda uku, daya a babbar kofar masallacin, wani a yankin kudancinn Masallacin, na uku inda masu ibada ke wanka kafin sallarsu.
Wani ganau ya kuma ce fashewar abubuwa guda ya gudana ne a masallacin da ke tsakiyar garin yayin sallar Juma’a.
Hukumomi suna tattara bayanai game da fashewar, in ji kakakin mukaddashin ma’aikatar harkokin cikin gidan gwamnatin Taliban Qari Saeed Khosti.
Ya Kuma kara da cewa, “Yan Taliban sun toshe dukkan hanyoyin da ke shiga masallacin da aka kai harin.”
Fashewar ta faru kwanaki kadan bayan da kungiyar Daesh ta yi ikirarin kai harin bam a masallacin ‘yan Shi’a dake birnin Kunduz da arewacin kasar Afghanistan, wanda ya kashe mutane akalla mutane 46.
Comments 1