Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (NECO) ta musanta cewa ta sake sanya ranar jarrabawar kammala sakandare ta SSCE da ta shirya yi a ranar Asabar 9 ga watan Yuli.
Ta bayyana cewa, maimakon haka, ta ba da cikakken mako guda ga daliban fomin hutu, daga ranar Juma’a 8 ga Yuli zuwa Laraba, 13 ga Yuli, 2022, don ba wa Musulmai adamar samun isasshen lokacin bikin na Sallah.
Wannan, a cewar shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NECO, Mista Azeez Sani a wata sanarwa da ya fitar a Minna, ya sabawa rade-radin da wasu ke yi na cewa hukumar ta tsara jarabawa a ranar 9 ga Yuli, 2022, wato ranar Sallah (Eid-Adha).
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar NECO na so ta bayyana cewa ba ta sanya ranar yin jarrabawar ba a ranar Asabar 9 ga watan Yuli, 2022. Ta bayar da cikakken mako daya domin hutu ga zasu zauna jarabawar,, wanda ya fara daga ranar Juma’a 8 ga watan Yuli zuwa Laraba 13 ga Yuli, 2022 don baiwa Musulmai damar samun isasshen lokacin bikin.
“Tun da an san mahimmancin bukukuwan addini, hukumar ta NECO ta kan samar da isassun tanadin irin wannan wajen kayyade ranakun jarrabawa”.
Idan Za a iya tunawa cewa jarrabawar shaidar kammala sakandare ta 2022 (SSCE) ga masu rubuta jarabawar, an fara ne a ranar 27 ga Yuni, kuma ana saran kammalawa a ranar 12 ga Agusta, 2022.
A wani labarin kuma na daban
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS a ranar Litinin din nan ta yi alkawarin sassauta takunkumin tattalin arziki da na kudi a kan kasar Mali.
Shugaban kungiyar ta ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou ne ya bayyana hakan a wajen rufe taron manema labarai na taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 61 a birnin Accra.
A cewar Brou, hukumomin kasar Mali sun dauki matakai wajen zartar da yarjejeniyar zabe da kuma kafa tsarin sa ido kan mika mulki.
Ya ce hukumomi sun kuma dauki matakin shirya sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Ya ce za a kawo karshen mika mulki a Mali a watan Maris din shekarar 2024 a cikin tsarin mika mulki na watanni 24.
Brou ya ce ECOWAS ta yanke shawarar dage duk wani takunkumin tattalin arziki da na kudi da aka sanya mata a ranar 9 ga watan Janairu.
“Wannan yana nufin, da gaske, rufe kan iyaka, daskarewar kadarorin kudi.
“An cire waannan takunkumin,” in ji shi,
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, ya kara da cewa jakadun kasashe mambobin ECOWAS a Mali za su koma Mali.
“Duk da haka, yayin da ake bukatar a sanya ido kan tsarin, shugabannin kasashe sun yanke shawarar ci gaba da sanya takunkumi na kowane mutum da kuma ci gaba da dakatar da Mali daga sassan cibiyoyin ECOWAS,” in ji shi.
(NAN)