Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, inda suka yi garkuwa da hakimin Panyam, Adamu Derwan.
A cewar shaidun gani da ido, ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan sarkin gargajiya a safiyar ranar Litinin inda suka dauke shi da karfi zuwa inda ba a sani ba kafin jami’an tsaro su isa wurin da lamarin ya faru.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP, Alfredo Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin daukar matakin gaggawa wajen zakulo wadanda suka yi garkuwa da basaraken, yayin da ake kira ga al’uma da su bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen kamo wadanda suka yi garkuwan.
Sarkin da aka sace na daga cikin wadanda suka fafata a zaben kujerar sarautar gargajiya ta Mishkaham Mwaghavul wadda ya sami nasara da kyar.
Zargin Tsige Ni: Har Yanzu Ina Da Karfin Iko – Kakakin Majalissar Dokokin Jihar Kogi
Satar Hakimin Panyam dai shi ne karo na biyar da ake garkuwa da shugabannin gargajiya a jihar cikin watanni shida da suka gabata.
A wani labarin kuma na daban.
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar na fama da matsanancin rashin lafiya, kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito.
Mai yiwuwa Janar din soja mai ritaya ya na fama da cutar hawan jini.
Rahotanni sun bayyana cewa an fitar da Abubakar daga Najeriya kimanin makonni uku da suka gabata domin yin jinya.
Da farko dai an dauke shi zuwa Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) amma yanzu yana wani asibiti a kasar Ingila (UK).
Abubakar ya samu rakiyar matar sa da kuma uwargidan tsohon shugaban kasa, Mai shari’a Fati Abubakar.
Surukin sa kuma gwamnan Neja, Abubakar Bello ya bar kasar bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC ya kai masa ziyara.
An kuma tattaro cewa shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) yana cikin koshin lafiya yayin da likitoci ke ci gaba da sa ido a kansa.