Jaridar The Cable ta labarto cewa; gobara ta tashi a gidansu tsohon shugaban kasar cif Olusegun Obasanjo da ke Ita-Eko a Abeokuta.
Wani dangin tsohon shugaban kasar ya shaida wa jaridar TheCable ewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da misalin karfe tara na dare, ko da yake gobarar ta shafi bangaren da matasa maza ke kwana ne kawai.
Rahotanni sun ce a gidan ne mahaifan Obasanjo suka yi rayuwarsu har suka rasu. Sannan gidan tsoho ne. Sannan ba shi ne babban gidan da Obasanjo ke rayuwa a ciki ba.
Sai dai bayanai sun ce tuni aka kashe gobarar.
Jaridar ta ce cif Obasanjo ba ya ma Nijeriya lokacin da lamarin ya faru, kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida daga taron kasashen Afirka da ya halarta a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.