By Ishaq Dabai
Da sanyin safiyar ranar Asabar wata gobara ta tashi a kasuwar Itobe inda ta lalata kadarori na miliyoyin Nairori wanda take a cikin ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi .
Kamar yadda wani shaidun gani da ido ya bayyana, cewa gobarar ta fara ne lokacin da injin janareta na wani dan kasuwa ya kone kurmus sakamakon haka wutar ta watsu zuwa saura shagunan dake cikin kasuwar inda ta lakume dukkan shagunan dake kusa dasu tare da lalata su.
Duk da cewa ba a rasa rai ba yayin bala’in, wanda abin ya faru a idanunsa ya ba da labarin cewa ‘yan kasuwa da yawa sun yi asara a hatsarin tashin gobarar.
Basaraken gargajiya na yankin, Onu Itobe, Alhaji Salihu Adaji yayin da yake mayar da martani ga bala’i ya bayyana cewa lamarin ya jefa ‘yan kasuwa da yawa a yankinsa zuwa kasuwar kwadago.
Sannan ya bukaci mutane masu hanu da shuni da su taimaka wa wadanda gobarar ta shafa da jari don sake fara kasuwancin su.