Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Legas Zata hana Sana’ar Acaɓa a wasu Ƙarin Ƙananan Hukumomi
Gwamnatin Jihar Legas ta tsawaita dokar hana Acaɓa da aka fi sani da Okada zuwa wasu kananan hukumomi hudu da wasu Gundumomin cigaba guda biyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ya zama dole ASUU ta biya diyya ga Ɗalibai kan ɓata masu lokaci – Minista
Kamar yadda aka tattaro, Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu, ya ba da umarnin aiwatar da cikakken aiki daga ranar 1 ga Satumba, na shekarar 2022.
Karin ƙananan Hukumomi da aka bayyana haramcin Okada baki daya, sun haɗa da karamar hukumar Kosofe, karamar hukumar Oshodi-Isolo, karamar hukumar Shomolu, da karamar hukumar Mushin.
Sauran sune Ikosi-Isherri, Agboyi-Ketu da Isolo da Bariga da Odi-Olowo.
A watan Mayu ne Sanwo-Olu ya haramta zirga-zirgar babura na kasuwanci a manyan tituna da kananan hukumomi shida da Gundumomin cigaba guda tara. Gwamnan ya sanar da cewa haramcin “babu ranar da za’a hana shi”.
Kananan hukumomi shida da gwamnan ya lissafa sune Ikeja, Surulere, Eti-Osa, Lagos Mainland, Lagos Island, da Apapa. Haramcin ya biyo bayan takunkumin da aka sanya a watan Fabrairun 2020 kan ayyukan baburan kasuwanci.
Sanwo-Olu ya ce gwamnati ta dauki wannan matakin ne bisa ga dokar sake fasalin bangaren sufuri na jihar na shekarar 2018 don gaggauta magance rudani da barazanar da ayyukan Okada ke haifarwa a yankunan da aka lissafa. Ya ce ‘yan sanda su aiwatar da wannan umarni ba tare da yin sulhu ba.
Ya ce, “Bayan nazarin da muka yi na takaita ayyukan Okada a kananan hukumomi shida na farko inda muka takaita su a ranar 1 ga Fabrairu, 2020, mun ga cewa barazanar ba ta ragu ba. Yanzu muna ba da umarnin dakatar da ayyukan Okada gaba daya a kan manyan tituna da gadoji a cikin wadannan kananan hukumomi shida da na kananan hukumominsu, daga ranar 1 ga Yuni, 2022.