Rahotanni sun bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama Doyin Okupe, tsohon Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zabenDan takarar shugaban kasa, na Jam’iyar Labour wato Peter Obi. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Rahotanni sun ce an kama Okupe ne ranar Alhamis a filin jirgin sama na Muritala Muhammed da ke Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dandazon Jama’ar Da Suka Fito A Onitsha Ya Nuna Cewa, Peter Obi Ne Zai Lashe Zabe — COSEYL
Daya daga cikin lauyoyinsa, Tolu Babaleye ne ya bayyana hakan a safiyar ranar Alhamis.
“Bayanin da ke zuwa gare ni yanzu shine, DSS sun kama Dr Doyin Okupe a filin jirgin sama na Legas akan hanyar sa ta zuwa Landan.
“Dalilin da ya sa a cewar majiyar shi ne, an nemi ya kawo hujjojin da ke nuna cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake shi daga shari’ar da aka yanke masa tare da biyan tarar da aka ci shi, tare da sanin duniya baki daya kuma aka ba shi izinin tafiya” in ji shi.
A wani labarin kuma, Shahararriyar Yar Wasan Tennis Ta Sami Juna Biyu
Tsohuwar wadda ta lashe manyan kofuna huɗu cikin shekara ɗaya a gasar tennis ta duniya ‘Grand Slam’, Naomi Osaka ta sanar da cewa a tana ɗauke da juna biyu a halin yanzu. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Osaka, ƴar asalin ƙasar Japan, wadda ta riƙe matsayi na ɗaya a jerin ƴan wasan tennis na duniya ta janye daga gasar ‘Australia Open’ a farkon wannan mako, kuma ba ta yi wasa ba tun watan Satumban shwkarar 2022.
Naomi Osaka ta ce “2023 za ta zamo shekara mai cike da darussa a gare ni”, sannan ta ce tana sa ran komawa harkokin wasan a shekarar 2024