Manyan hafsoshin sojojin Koriya ta Kudu sun ce Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami da ba a tantance ba a cikin ruwan tekun gabashin kasar a ranar Asabar.
Harba makamin na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki uku bayan da Pyongyang ta harba wani makami mai linzami, yayin da ake ci gaba da fargaban cewa za ta iya yin gwajin makamin nukiliya.
“Koriya ta Arewa ta harba wani shu’umin makami Mai linzami guda ɗaya zuwa gabar Tekun dake Gabashin kasar nan,” in ji manyan hafsoshin sojojin Seoul, yayin da suke magana kan Tekun Japan.
Jami’an tsaron gabar tekun Japan, sun ambato bayanai daga ma’aikatar tsaronta, sun ce Koriya ta Arewa ta harba wani abu “mai yiwuwa ya zama makami mai linzami,” kuma ta gargadi jiragen ruwanta da su yi taka tsan-tsan.
Ƙaddamarwar ya kasance gwajin makamin na 15 daa ƙasar ta Korea ta Arewa ta yi, Wanda Kuma akayi amannar cewa ta na da makaman nukiliya ya zuwa yanzu.
KARANTA Wannan Labarin: Attajiri Todd Boehly ya zama Sabon Mai Mallakin Chelsea
A ranar Laraba, Koriya ta Arewa ta yi gwajin abin da Seoul da Tokyo suka ce makami mai linzami ne, ko da yake kafofin yada labaran gwamnatin Pyongyang da ke ba da rahoto kan gwajin makaman ba su yi tsokaci kan taron ba.
Duk da takunkumin kasa da kasa kan shirye-shiryenta na makamai, Koriya ta Arewa ta kara zage damtse a wannan shekarar tare da yin watsi da tayin kasar Amurka.
Gwajin na ranar Asabar ya zo ne ‘yan kwanaki kafin a rantsar da sabon shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol a ranar Talata mai zuwa.
Na futuhi
Masoyin shehu