By Ishaq Dabai
Babbar kotun tarayya dake zama ta a Abuja, a ranar Litinin, ta bada umurnin da a gaggauta sakin fasfon na kasa da kasa na tsohon gwamnan jihar Ribas, Dokta Peter Odili, wanda hukumar shige da fice ta Najeriya NIS ta kwace. Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya gabatar da shi, inda yace babu wata hujja ta shari’a kan matakin da hukumar NIS ta dauka kan tsohon gwamnan.
Odili, wanda ya jagoranci harkokin jihar Ribas daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya garzaya kotu don kalubalantar kwace fasfot din sa na kasa da hukumar NIS ta yi.
Ya shaida wa kotun cewa fasfot din nasa mai lamba B50031305, jami’an hukumar NIS sun kwace shi a ranar 20 ga watan Yuni saboda wani dalili da ba a bayyana ba, jim kadan bayan ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja.inda yace tun da farko hukumar NIS ta ki sakin masa fasfo din.
A cikin takardar rantsuwa mai sakin layi 8 shi da kansa, tsohon gwamnan, yace ya sauka a filin jirgin sama daga Burtaniya inda ya tafi don duba lafiyarsa ta yau da kullun.Odili ya shaidawa kotun cewa ya biya kuma ya mika takardunsa ga jami’in daya tafi da shi kuma ya kasa mayar da ita.Wanda aka kawo a cikin wadanda ake kara a cikin lamarin sune hukumar NIS da Kwanturola Janar din ta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hukumar ta NIS ta gabatar da karar a gaban kotun, inda taci gaba da cewa matakin nata ya samo asali ne daga umurnin Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa EFCC, wanda tace ta sanya tsohon gwamnan a cikin jerin wanda zasu sanya ido a kansa.