By Ishaq Dabai
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan a ranar Laraba ya rantsar da Agom Jarigbe a matsayin wanda zai maye gurbin Stephen Odey.
Jarigbe wanda dan jam’iyyar PDP yana ta shari’ar da Odey akan wanda shine ainihin dan takarar jam’iyyar na Cross River ta Arewa.
Jarigbe wanda ya yi rantsuwar zama Sanata bayan nasarar da ya samu a Kotun Koli.
Idan zaku iya tunawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC itace ta gudanar da zaben Cross River ta Arewa bayan rasuwar Sanata Rose Oko.