Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Zamfara ya ba da umarnin dawo da hanyar sadarwar tarho a Gusau, babban birnin jihar
Tun daga watan Satumbar da ya gabata ne aka yanke aiyukan sadarwa a cikin jihar, a matsayin wani bangare na matakan magance Yan bindiga a fadin jihar.
Amma a cikin wata sanarwa, Zailani Bappa, mai ba gwamnan shawara na musamman kan wayar da kan jama’a, kafofin watsa labarai da sadarwa, ya bayyana cewa, Matawalle ya ce, ya kamata a maido da hanyar sadarwa daga yau Juma’a a garin Gusau.
Sanarwar tayi nuni da cewa, “Gwamnan ya ba da umurnin dawo da aiyukan sadarwa a babban birnin jihar Gusau, kawai daga yau Juma’a, 1 ga Oktoba, 2021.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta dakatar da Taron Wakilan NUJ
“Maido da kafofin sadarwar a Babban Birnin Jihar ya zama mai mahimmanci bayan gagarumar nasarar da aka samu a yakin da ake yi da Yan bindiga a jihar, da kuma rage wahalhalun da bangarorin gwamnati, da Kamfanoni masu zaman kansu su ke fuskanta.” Inji sanarwar.
“Gwamna Matawalle ya yi alƙawarin cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a fadin jihar.”
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya yi afuwa ga fursunoni 18 da aka daure a gidajen kurkukun dake jihar.sannan Akeredolu ya kuma daure wasu fursunoni 26 da aka yan kewa hukuncin kisa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai, Richard Olatunde, ya sanya wa hannu, Olatunde ya ce wannan karimcin da gwamnan yayi shine don tunawa da ranar samun ‘yancin kai na wannan shekarar.
Sanarwar tace “A cikin yin amfani da ikon na sakin layi (d) na ƙaramin sashe na (1) na sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya,na shekarar 1999 kamar yadda aka gyara, Gwamnan Jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, yayiwa Fursunoni 18 a fuwa wadanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan kaso.
“Gwamnan ya kuma daure wasu fursunoni ashirin da shida 26 wadanda kotuna daban daban na jihar suka yanke wa hukuncin kisa.
An saki wadanda aka yankewa hukuncin ne bayan sun nuna nadama da kuma halaye masu kyau a cibiyoyin gidan gyaran hali ”Yayin daya umarce su dasu kasance masu kyawawan halaye da yin rayuwa ba tare da aikata laifi ba ana gaba, gwamnan ya bukaci jama’a da kada su nuna musu wariya yayin da suke sake komawa gida cikin al’umma.
Comments 1