Wani jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari a arewacin Ivory Coast yayin da yake aikin leken asiri kusa da kan iyaka da kasar Burkina Faso.
An fara gudanar da bincike don gano musabbabin faduwar jirgin, in ji ma’aikatar tsaron kasar.
Kazalika Ma’aikatar ta ce,Duk Ma’aikatan jirgin guda biyar sun mutu, sanadiyar hadarin jirgin da ya afku a ranar Juma’ar data gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: An bude Makarantun da aka samu barkewar cutar Kwalara a Jigawa
Tun da fari dai, ma’aikatar ta ba da rahoton cewa, jirgin mai saukar ungulu ya bace kafin daga bisani su fitar da sanarwar da take tabbatar da hadarin jirgin a yau Asabar.
Idan za’a iya tuna wa, Yankunan kan iyakar kasar Ivory Coast da na Burkina Faso sun zama wuraren rashin tsaro a cikin shekarar da ta gabata.
Wannan ya biyo bayan hare -hare da dama daga masu kishin Islama, da ake kyautata zaton cewa, suna da alaka da kungiyar Al-Qaeda.