Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya isa Abuja, domin ganawa da kungiyar Kiristocin Najeriya, wato CAN. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Dattawa Ta Yi Sammacin Ministar Kudi Kan Wasu Kudade Da Aka Cusa A Kasafin Kudi
Ya rubuta: “Na isa wurin taron tattaunawa da kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a Abuja.”
A baya ma kungiyar CAN ta gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
A wani labarin kuma, Najeriya Da Kanada Za Su Iya Yin Abubuwa Da Yawa Tare — Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Najeriya da Canada za su iya yin abubuwa da yawa tare ta hanyar inganta kasuwanci, zurfafa hadin gwiwa a fannin ilimi, ci gaba da tattaunawa kan batutuwan sauyin makamashin duniya da sauyin yanayi, da dai sauransu.
Wannan shi ne babban taron da Osinbajo ya yi da mataimakiyar firaministan kasar Canada, Chrystia Freeland, a Ottawa, babban birnin kasar Arewacin Amirka a ranar Litinin