Shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda na kasa (PSC), Musiliu Smith ya yi murabus daga mukaminsa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, masu fada aji a hukumar sun bukaci Smith ya yi murabus kuma ya amince da wannan bukata
KARANTA WANNAN LABARIN: Dan Wani Sanata Ya Mutu A Babban Birnin Tarayya Abuja
Wata majiya mai tushe a hukumar ta shaida wa Majiyar Dimokuradiyya cewa Smith, tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, ana sa ran mika shi ga mai shari’a Clara Ogunbiyi mai murabu dake wakiltar bangaren shari’a a hukumar.
Kakakin hukumar Ikechukwu Ani shi ma ya tabbatar wa wakilin Majiyar Mu murabus din ta wayar tarho.
An samu sabani tsakanin hukumar da ofishin Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar nan, kan ko wace hukuma ce ke da hakkin gudanar da aikin daukar sabbin Jami’an yan sanda a fadin kasar nan.
Hukumar ta PSC ta yi shelan daukar ma’aikata ga ‘yan sanda kuma ta bukaci masu sha’awar su ziyarci shafin yanar gizon rundunar don nema aikin.
Sai dai rundunar ‘yan sandan a wata sanarwa da ta fitar ta bukaci jama’a da su yi watsi da sanarwar, inda ta nanata cewa aikin daukar sabbin jami’an yan sanda ya rataya ne a wuyan rundunar.
A WANI LABARI KUMA: Ana Zargin Wani Dalibi Ya Kashe Kansa A Hannun Hukumar Civil Defence
Wani matashi mai suna Musa David dan shekara ashirin da biyar a duniya a Sashen koyan harkokin kudi da aikin Banki da a Waziri Umaru Federal Polytechnic (WUFP) Birnin Kebbi ya kashe kansa.
David ya kashe kansa ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC a Birnin Kebbi.