Wasu ‘yan bindiga da sanyin safiyar yau Lahadi sun kai hari hedikwatar’ yan sanda da ke Unwana na karamar hukumar Afikpo ta Arewa a jihar Ebonyi, inda suka kashe ‘yan sanda uku da ke bakin aiki.
‘Yan bindigar da aka ce sun kai farmaki da misalin karfe 2 na safe, sun kashe dan sanda daya, da sifetoci guda biyu, kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito.
Wata majiya daga yankin da ta zanta da majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta lgano cewa, ‘yan bindigar sun rufe fuskokinsu yayin Kai harin.
Ya ce, “Sun kashe‘ yan sanda uku kuma ‘yan sandan sun kashe daya daga cikin‘ yan bindigar” inji majiyar
KARANTA WANNAN LABARIN: A shirye nake nayi aiki da Shekarau, innji Kwankwaso
“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na safe, babu wanda ya san hanyar da suka fito, Amma sun yi harbe -harbe na kusan mintuna 10.l”
“A halin yanzu babu wani bayani da za a sani, game da ko sun lalata, ko sace wani abu daga ofishin‘ yan sanda.”
Yunkurin samun tabbaci na ‘rundunar yan sanda jihar ya ci tura, saboda mai magana da yawun’ rundunar DSP Loveth Odah, ta kasa amsa kiran da aka yi mata, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Comments 1