‘Yan bindiga a ranar Litinin sun kai hari gidan yarin garin Owerri dake jihar Imo inda suka tseratar da fursuna fiye da 1, 500 kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana.
Maharan har wala yau sun kari hari a Hedikwatar ofishin ‘yan sandan garin Owerri, inda suka kona baki daya motocin da aka ajiye a hedikwatar ofishin ‘yan sandan.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa maharan har wala yau sun tseratar da wadanda ake zargi aka kuma ajiye a ofishin ‘yan sandan domin bincike.
Majiyarmu ta ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 1 na dare inda suka ci karensu ba babbaka har zuwa karfe 3 na dare a ranar Litinin.
Bayanai sun ce kafin ma su kai harin sai da suka kwashe minti talatin suna rera wake a Roundabout na gidan gwamnati.
Bayan sun balla gidan yarin da abubuwa masu fashewa, sun nemi fursunonin kowa ya gudu ya tafi gida.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da faruwar lamarin.