Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da kisan mutane uku da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyukan Ebbo da Ndagbegi da ke karamar hukumar Lavun a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Monday Kuryas ne ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna a yau Lahadi.
Kuryas ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 5 na safe lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari kauyen.
A cewarsa, an tura tawagar ‘yan sanda da sojoji zuwa yankin inda suka fara farautar ‘yan ta’addan da nufin zakulo barayin.
“Muna kira ga mazauna yankin da su taimaka wa jami’an tsaro da aka tura da ingantattun bayanai da za su taimaka wajen kama barayin da ke tsakaninsu,” in ji kwamishinan ‘yan sandan.